MATSAYIN SHARI’A A AYYUKAN ADABIN ABUBAKAR IMAM
Loading...
Date
Authors
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
Abstract
TSAKURE
Shari’a ita ce ginshi}in samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar
Hausawa. Wanda bisa ga dukkan alamu shi ya sa Abubakar Imam ya yi
}o}arin kawo ta cikin rubuce-rubucensa. Wannan bincike mai taken
“Matsayin Shari’a a Ayyukan Abubakar Imam .“ Wanda ya shafi Littafin
Ruwan Bagaja da Magana Jari Ce I-III. An raba wannan aikin zuwa babi
shida wato babuka shida don gudanar da wannan aikin. An kawo
gabatarwa wanda yake sharar fage ne sai aka kawo manufar bincike da
dalilin gudanar bincike da hanyoyin da aka bi domin samun nasarar
gudanar da wannan bincike sai ra’in bincike. Sai aka yi bitar ayyukan da
suka gabata. Sai aka kawo Abubakar Imam da ayyukansa inda aka kawo
ta}aitaccen tarihinsa da kuma ayyukansa wa]anda suka ha]a da ayyukan
hukuma da na adabi. Sannnan aka tattauna shari’a a al’ummar Hausawa,
sai bayyana ma’anar shari’a da rabe-raben shari’a da hanyoyin gudanar
da shari’ar gargajiya ta Hausawa. Daga nan sai aka kawo shari’ar
Musulunci da shari’ar zamani da kuma matsayin shari’a a rayuwar
Hausawa. Haka ma an yi nazarin }umshiya da hikimar da ke cikin shari’a a
cikin ayyyukan adabin Abubakar Imam . Tare da kawo misalan inda aka
gudanar da shari’a a cikinsu. A nan ne aka dubi laifuffuka da hukunce
hukuncensu. Wa]anda suka shafi sata da }azafi da zamba cikin aminci da
saye ko ajiyar kayan sata da cin hanci da rashawa da sauransu. A }arshe
aka kawo kammalawa da sakamakon bincike sai kuma manazarta.
ABSTRACT
The tittle of this research is “The Position of Law In Abubakar Imam’s
Litereture.” The work has been classified into six chapters. The general
introduction. Where the objectives of the study. Scope and limitation of
research, theory and methodology adopted in under taking the research
were discuss. The review of relevant litereture and also brief history of
the authour of the books i.e Abubakar Imam and his books. The
traditional law in Hausa society which touched the meaning and the types
of law, the position of law and the ways of conducting the traditional law
in the life of Hausa people, the islamic, the mordern law and the position
of law in Hausa society where discussed. Further more the content and
wisdom of law in position of Abubakar Imam’s litereture i.e from book of
Ruwan Bagaja and Magana Jari Ce I-III with examples of of places where
laws was conducted. The laws includeshistory, law of succession,
identifying the law and their rullings. Which includes murder, thief,
mischief, buying or keeping thieves property briebry and corruption
wisdom and so on. Lastly is the conclusion and recomendation a detailed
reference is given on the materials consulted.
