KU[I A TUNANIN BAHAUSHE: DUBA A CIKIN WASU SASSAN ADABIN BAKA NA HAUSA
Loading...
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
TSAKURE
Wannan bincike mai suna, ‘Kuxi A Tunanin Bahaushe:Duba a Cikin Wasu Sassan
Adabin Baka na Hausa’ bincike ne da ya shafi shiga cikin sarrafaffen adabin baka na
Bahaushe domin fito da falsafar rayuwarsa wanda ya shafi mu’amala da kuxi. Binciken
ya nuna yadda kuxi suke yin tasiri wajen gudanar da rayuwar Bahaushe. Haka kuma an
fito da yadda kuxi suke sauya tunanin wasu mutane a cikin harkokin yau da kullum.
Binciken ya nuna yadda kuxi suke haddasa ayyukan ta’addanci a cikin al’umma da
yadda wasu ke amfani da kuxi wajen yin kyawawan ayyuka. An yi amfani da waqoqin
baka da tatsuniya da qissa da karin magana da kirari wajen fito da tunanin Bahaushe
game da kuxi. An xora wannan bincike a kan ra’in madubin qyallaro al’adu. Mai
bincike ya yi amfani da wannan ra’i ne domin qyallaro al’adar kuxi da ke cikin adabin
bakan Bahaushe. A qarshe binciken ya fito da sakamakon bincike a taqaice, wataus
yadda Bahaushe ya gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali da }aunar juna kafin
samuwar kuxi da kuma yadda ya yi amfani da abubuwan da ke cikin muhallin sa wajen
biyan muhimman buqatun rayuwarsa. Haka kuma samuwar kuxi ya kawar da tsohuwar
al’adar nan ta hur-hure a wajen kasuwanci. Daga cikin sakamakon binciken, akwai
yadda al’umma suke kallon maikuxi da kuma yadda shi yake kallon kansa. Sannan da
irin rawar da yake takawa wajen taimakon talakawa a cikin al’umma. Samuwar kuxi
sun inganta ayyukan qwadago da kasuwanci da bunqasar tattalin arzikin Bahaushe. Har
wa yau, binciken ya gano illar kuxi wanda ya haxa da zalunci da da yaudara da kisan
kai. Haka nan binciken ya fahimci cewa Bahaushe ya sauya alakar rayuwarsa zuwa ga
kuxi. Wanda ya yi sanadiyyar watsi da nagarta da halayen qwarai. Binciken ya gano
cewa, zafin neman ba ya kawo samu. Mallakar kuxi nufin Alla ne. Qwazo da dabara da
wayau duk ba su tara kuxi. Daga qarshe an ba da shawarwari na musamman waxanda
za su taimaka wa duk wani mai sha’awar nazarin al’ada a cikin adabin Hausawa.
5.2 Sakamakon bincike ............................................................................................ 154
5.3 Shawarwari ........................................................................................................ 159
5.4 Naxewa ............................................................................................................. 160
MANAZARTA ............................................................................................................ 160
ABSTARCT
This research work titled, ‘Kuxi A Tunanin Bahaushe:Duba a Cikin Wasu Sassan
Adabin Baka na Hausa’ was a research based on Hausa Oral Literature. The research
was aimed at bringing out the philosophical thoughts of Hausa People in relation to
money. The research shows the influence of money on the day-to-day activities of
Hausa man. The research also shows the negative impact of money on the spread of
terrorism in the society. It also shows how some people make use of money positively in
assisting others. The research shows how Hausa man lived a peaceful life before the
advent of money. After the advent of money so many changes takes place which include
change from trade by batter to the use of money. The research findings shows how
wealthy people in the society assists the poor and the needy..It also reveals how rich
man perceived himself and how he is equally perceived by others. Hausa people have
changed their societal value, and re-directed it towards money, thus, neglecting moral
values such as honesty, integrity, etc .It shows that acquiring money is not by hard
working, dedication but God’s willing. The research employed the use of Hausa oral
song, folktales story, Proverbs, and praise song. This research was based on
Referential Theory of Culture. In conclusion of this study, a summary of the work,
findings and recommendation to scholars who are interested in researching into this
area were given.
