UNGUWANNIN BIRNIN ZAZZAU DA KEWAYE: NAZARI A KAN IRE IREN SANA’O’IN DA AKE YI CIKINSU JIYA DA YAU
Loading...
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
Abstract
TSAKURE
Manufar wannan bincike ita ce fito da tarihi da asalin unguwannin da
sana’o’i suka kafa a birnin Zariya da kuma dalilan kafa su. Wannan shi
ya sa aka yi wa binciken taken: Unguwannin Birnin Zazzau Da Kewaye:
Nazari A Kan Ire-iren Sana’o’in Da Ake Yi Cikinsu Jiya Da Yau. Nazarin
ya fito da tsofaffi da sababbin unguwannin birnin Zariya. A cikin aikin
bayan gabatarwa, an yi waiwaye kan tarihin birnin Zariya ta hanyar
gabatar da tsofaffi da sababbin ungunwannin garin. An kalli tsofaffin
unguwanni kamar Unguwar Alfadarai da Unguwar Alqali da Unguwar
Amaru da Unguwar Babban Dodo. Haka kuma an tattauna a kan
sababbin unguwanni kamar Tudun Wada da Sabon Gari da Samaru da
kuma Wusasa. Bugu da qari, binciken ya gabatar da sana’o’in da suka
yi fice a dukkan unguwannin da ke birnin Zariya da kewaye, kamar
sana’ar qira a unguwar Qarfe da sana’ar xinki a unguwar Madaka da
sana’ar aski a unguwar Magajin Aska da sana’ar sirdin dawaki a
unguwar Sirdi da kuma sana’ar noma da kiwo a unguwar Samaru. A
qarshe, aikin ya gano cewa birnin Zariya wuri ne na matattarar
masana’antu na gargajiya, kuma akwai alaqa mai qarfi a tsakanin masu
gudanar da waxannan sana’o’i.
ABSTRACT
The aim of this research is to trace the history of wards that were
established as a result of craftsmanship in Zaria Metropolis as well as the
reasons behind their creation. Hence the research is entitled ‘Zaria
Metropolis and Environs: A Study on Ward-Crafts Yesterday and Today’,
which studied the old and new wards in Zaria Metropolis. After a general
introduction, the study presented a brief history of Zaria Metropolis by
way of deliberating on the old wards such as that of Alfadarai, Alqali,
Amaru as well as the Area of Babban Dodo. On the other hand, new wards
such as Tudun Wada, Sabon Gari, Samaru and Wusasa areas were
presented. Nonetheless, prominent crafts practiced yesterday and today in
the wards and Zaria Metropolis were discussed. Crafts such as
blacksmithing in the ward of Qarfe, Couture in the ward of Madaka,
barbing in the ward of Magajin Aska, saddle making in the ward of Sirdi,
and farming in the ward of Samaru were all discussed. Finally, the research
concludes that Zaria is an important metropolis with numerous local
industries having strong ties among the craftsmen.
