UNGUWANNIN BIRNIN ZAZZAU DA KEWAYE: NAZARI A KAN IRE IREN SANA’O’IN DA AKE YI CIKINSU JIYA DA YAU
| dc.contributor.author | YUSUF MUKHTAR (ADM. NO.: 13210106004) | |
| dc.date.accessioned | 2026-02-13T11:00:45Z | |
| dc.date.issued | 2019-05-25 | |
| dc.description.abstract | TSAKURE Manufar wannan bincike ita ce fito da tarihi da asalin unguwannin da sana’o’i suka kafa a birnin Zariya da kuma dalilan kafa su. Wannan shi ya sa aka yi wa binciken taken: Unguwannin Birnin Zazzau Da Kewaye: Nazari A Kan Ire-iren Sana’o’in Da Ake Yi Cikinsu Jiya Da Yau. Nazarin ya fito da tsofaffi da sababbin unguwannin birnin Zariya. A cikin aikin bayan gabatarwa, an yi waiwaye kan tarihin birnin Zariya ta hanyar gabatar da tsofaffi da sababbin ungunwannin garin. An kalli tsofaffin unguwanni kamar Unguwar Alfadarai da Unguwar Alqali da Unguwar Amaru da Unguwar Babban Dodo. Haka kuma an tattauna a kan sababbin unguwanni kamar Tudun Wada da Sabon Gari da Samaru da kuma Wusasa. Bugu da qari, binciken ya gabatar da sana’o’in da suka yi fice a dukkan unguwannin da ke birnin Zariya da kewaye, kamar sana’ar qira a unguwar Qarfe da sana’ar xinki a unguwar Madaka da sana’ar aski a unguwar Magajin Aska da sana’ar sirdin dawaki a unguwar Sirdi da kuma sana’ar noma da kiwo a unguwar Samaru. A qarshe, aikin ya gano cewa birnin Zariya wuri ne na matattarar masana’antu na gargajiya, kuma akwai alaqa mai qarfi a tsakanin masu gudanar da waxannan sana’o’i. ABSTRACT The aim of this research is to trace the history of wards that were established as a result of craftsmanship in Zaria Metropolis as well as the reasons behind their creation. Hence the research is entitled ‘Zaria Metropolis and Environs: A Study on Ward-Crafts Yesterday and Today’, which studied the old and new wards in Zaria Metropolis. After a general introduction, the study presented a brief history of Zaria Metropolis by way of deliberating on the old wards such as that of Alfadarai, Alqali, Amaru as well as the Area of Babban Dodo. On the other hand, new wards such as Tudun Wada, Sabon Gari, Samaru and Wusasa areas were presented. Nonetheless, prominent crafts practiced yesterday and today in the wards and Zaria Metropolis were discussed. Crafts such as blacksmithing in the ward of Qarfe, Couture in the ward of Madaka, barbing in the ward of Magajin Aska, saddle making in the ward of Sirdi, and farming in the ward of Samaru were all discussed. Finally, the research concludes that Zaria is an important metropolis with numerous local industries having strong ties among the craftsmen. | |
| dc.identifier.uri | https://repository.udusok.edu.ng/handle/123456789/323 | |
| dc.language.iso | other | |
| dc.publisher | DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES | |
| dc.title | UNGUWANNIN BIRNIN ZAZZAU DA KEWAYE: NAZARI A KAN IRE IREN SANA’O’IN DA AKE YI CIKINSU JIYA DA YAU | |
| dc.type | Other |
