NAZARI A KAN RAYUWA DA WAQOQIN MALAM ALIYU UMAR KAFIN HAUSA
Loading...
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
Abstract
TSAKURE
Wannan bincike ya dubi tarihi da waqoqin Malam Aliyu Umar Kafin Hausa ne.
Manufar binciken ita ce yin nazarin waqoqinsa tare da taskace su. An xora tubalin
binciken a kan tsarin babuka, daga babi na xaya wanda yake a matsayin gabatarwa,
zuwa babi na biyu da na uku da na huxu. A cikin wannan binciken an yi bitar ayyukan
magabata da tarihin rayuwar marubucin tare da sharshin wasu zavavvun waqoqinsa
guda takwas waxannan suka haxa da ‘Waqar Renon Juna’ da ‘Waqar Gyara Kayanka’
da waqar ‘Uwa da Uba’ da waqar ‘ Mace Tagari’ da waqar ‘ Road Safety’ da waqar ‘
Illolin Talla’ da waqar ‘ Xaliban Miga’ da waqar ‘Xaliban Imamu Hassan’. Daga
qarshen an gano cewa jigogin waqoqin da marubuci ya rubuta sun taimaka wajen
faxakar da al’umma a fannonin rayuwar yau da kullum. Sannan angano cewa mawaqin
ya yi amfani da salo miqaqqe mai armashi kuma sabo, domin salon ya tafi kai tsaye
kuma yana da sauqin ganewa. Har ila yau an gano cewa marubucin ya yi amfani da zubi
da tsari cikin waqoqin ta hanyar jeranta tunaninsa wanda babu kwan – gaba – kwan
baya, kuma baitocin waqoqin na da danganta da xangwayensu.sun kuma qunshi
manufofi don cikar ma’ana Sannan an kawo jawabin kammalawa da sakamakon bincike
da matsaloli da kuma shawarwari a taqaice.
ABSTRACT
The research work focused on the biography and poetic works of Malam Aliyu Umar
Kafin Hausa. The hypothesis behind this work is to make a thorough investigation into
the poems of Malam Aliyu Umar together with the aim of preserving them. The
research work was composed on chapters, from chapter one of introduction to chapter
two, three and four. Literature review, biography of Malam Aliyu Umar and
investigation into some of his poems like ‘ Renon Juna’, ‘Gyara Kayanka’, ‘ Uwa da
Uba ‘, ‘ Mace Tagari’, ‘Road Safety’, ‘Illolin Talla’, Xaliban Miga’ and Xaliban Imamu
Hassan’ dicussed in those chapters. The work is purposely to bring to a relevant and
reasonable degree the resoucess available in Malam Alyu Umar work for profitable use
in generality and in a particular at levels of education. Finally the work has been a
reflections in brief of discoveries from a stylistic analysis of the works involving the
various linguistics features used un the poems in such away that they amount to poetic
idiosyncracy and state the extent to which other factors such as extra-linguistics features
of stylistic significance, the poets involvement in the universe of the poems and possible
use of idiosyncratic lexicon affect the interpretation of the work.
