NAZARIN HAUSAR WASU RUKUNAN ‘YAN KASUWA A GARIN SAKKWATO
Loading...
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
Abstract
TSAKURE
Wannan bincike ya yi nazarin nau’o’in wasu kare-karen Hausar rukunan
‘yankasuwa a garin Sakkwato. Manufar binciken ita ce, tabbatar da wanzuwar
karin rukunin Hausar wasu ‘yankasuwa a hul]ar kasuwanci a garin Sakkwato. Tare
da yin nazari na }wa}}wafi kan sababbin ma’anonin da suke amfani da su. A
wannan bincike an yi amfani da hanyoyin tattaro bayanai wa]anda suka ha]a da:
Tattaunawa da lura ta kai tsaye, don gwada hasashen da aka yi a kan lafuzzan da
suke amfani da su a muhallan aiwatar da kasuwanci. An tattaro kalmomi da yankin
jumloli da jumloli don nazarin yadda suke amfani da su, da tabbatar da wanzuwar
karin rukunin harshen nasu. An yi amfani da Ra’in Vangarorin Kalmomi (Lexical
Pragmatic Theory (LPT) wanda Blutner ya samar a shekarar 2000, domin ya yi
jagoranci wajen nazartar ma’ana ta hanyar la’akari da gundarin rubutu. Saboda
haka, yana da inganci wajen gabatar da bayanai. Bayan haka, ra’in na mayar da
hankali zuwa ga nazartar sauyin ma’ana da akan samu ta hanyar la’akari da
vangarorin kalma (Lexical Pragmatic Approach). Wannan ra’ayi ya tafi kan cewa,
ana nazartar kalmomin harshe cikin salo na musamman tare da ba su ma’anoni ta
hanyar la’akari da kanun batu da ake magana a kansa. Binciken ya gano cewa,
wasu rukunan ‘yankasuwar garin Sakkwato na amfani da wasu ma’anoni na
musamman wa]anda ba kowa ke iya gane su ba sai ]an rukuninsu. Wani
sakamakon binciken kuma ya gano cewa ma’anonin da suke amfani da su sun samu
ne daga fa]a]a ma’ana da }ir}ira da kuma sarrafa kalmomin aro, domin samun yin
sadarwa kamar yadda ta dace a tsakaninsu. Haka kuma, binciken ya gano yadda
sauyawar ma’ana ta kasance sakamakon fa]a]a ma’anar kalmomi.
ABSTRACT
This study investigated the variety of registers used by some occupational groups
in Sokoto Metropolis. The objective of this research is to evidently proved the
existence of this registers. The research examined the meaning of the registers
critically. This research is a product of primary data collection through interview
and direct observation of traders’ utterances in their various locations. Some
related words, phrases and sentences were selected and studied, in order to
evidently proved the existence of this registers. The Lexical Pragmatic Theory
(LPT) identified by Blutner (2000) was used as guidelines to critically analyses
meaning through the context and therefore is effective in the representation of
concepts. It also focuses on the study of meaning change in line with lexical
pragmatic approach. The approach assumes that lexical items of a language are
analyzed systematically and interpreted according to a particular context. The
findings of this research discovered that, Hausa traders in Sokoto use some
peculiar registers in their commercial communication which their meaning can not
be understood by other groups. Another finding of the research revealed that,
some Hausa traders in Sokoto used three strategies to form their registers. This
include, semantic extension, coinage and borrowings in order to communicate
properly within their social group. The research discovered some semantic
changes in extended meaning.
