NAZARIN HAUSAR WASU RUKUNAN ‘YAN KASUWA A GARIN SAKKWATO
| dc.contributor.author | MUHAMMAD MUSTAPHA UMAR (ADM. NO: 14310106001) | |
| dc.date.accessioned | 2026-02-13T11:20:15Z | |
| dc.date.issued | 2019-03-11 | |
| dc.description.abstract | TSAKURE Wannan bincike ya yi nazarin nau’o’in wasu kare-karen Hausar rukunan ‘yankasuwa a garin Sakkwato. Manufar binciken ita ce, tabbatar da wanzuwar karin rukunin Hausar wasu ‘yankasuwa a hul]ar kasuwanci a garin Sakkwato. Tare da yin nazari na }wa}}wafi kan sababbin ma’anonin da suke amfani da su. A wannan bincike an yi amfani da hanyoyin tattaro bayanai wa]anda suka ha]a da: Tattaunawa da lura ta kai tsaye, don gwada hasashen da aka yi a kan lafuzzan da suke amfani da su a muhallan aiwatar da kasuwanci. An tattaro kalmomi da yankin jumloli da jumloli don nazarin yadda suke amfani da su, da tabbatar da wanzuwar karin rukunin harshen nasu. An yi amfani da Ra’in Vangarorin Kalmomi (Lexical Pragmatic Theory (LPT) wanda Blutner ya samar a shekarar 2000, domin ya yi jagoranci wajen nazartar ma’ana ta hanyar la’akari da gundarin rubutu. Saboda haka, yana da inganci wajen gabatar da bayanai. Bayan haka, ra’in na mayar da hankali zuwa ga nazartar sauyin ma’ana da akan samu ta hanyar la’akari da vangarorin kalma (Lexical Pragmatic Approach). Wannan ra’ayi ya tafi kan cewa, ana nazartar kalmomin harshe cikin salo na musamman tare da ba su ma’anoni ta hanyar la’akari da kanun batu da ake magana a kansa. Binciken ya gano cewa, wasu rukunan ‘yankasuwar garin Sakkwato na amfani da wasu ma’anoni na musamman wa]anda ba kowa ke iya gane su ba sai ]an rukuninsu. Wani sakamakon binciken kuma ya gano cewa ma’anonin da suke amfani da su sun samu ne daga fa]a]a ma’ana da }ir}ira da kuma sarrafa kalmomin aro, domin samun yin sadarwa kamar yadda ta dace a tsakaninsu. Haka kuma, binciken ya gano yadda sauyawar ma’ana ta kasance sakamakon fa]a]a ma’anar kalmomi. ABSTRACT This study investigated the variety of registers used by some occupational groups in Sokoto Metropolis. The objective of this research is to evidently proved the existence of this registers. The research examined the meaning of the registers critically. This research is a product of primary data collection through interview and direct observation of traders’ utterances in their various locations. Some related words, phrases and sentences were selected and studied, in order to evidently proved the existence of this registers. The Lexical Pragmatic Theory (LPT) identified by Blutner (2000) was used as guidelines to critically analyses meaning through the context and therefore is effective in the representation of concepts. It also focuses on the study of meaning change in line with lexical pragmatic approach. The approach assumes that lexical items of a language are analyzed systematically and interpreted according to a particular context. The findings of this research discovered that, Hausa traders in Sokoto use some peculiar registers in their commercial communication which their meaning can not be understood by other groups. Another finding of the research revealed that, some Hausa traders in Sokoto used three strategies to form their registers. This include, semantic extension, coinage and borrowings in order to communicate properly within their social group. The research discovered some semantic changes in extended meaning. | |
| dc.identifier.uri | https://repository.udusok.edu.ng/handle/123456789/324 | |
| dc.language.iso | other | |
| dc.publisher | DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES | |
| dc.title | NAZARIN HAUSAR WASU RUKUNAN ‘YAN KASUWA A GARIN SAKKWATO | |
| dc.type | Thesis |
Files
Original bundle
1 - 1 of 1
Loading...
- Name:
- Nazarin Hausar Wasu Rukunan 'Yankasuwa a Garin Sakkwato (1).pdf
- Size:
- 271.19 KB
- Format:
- Adobe Portable Document Format
License bundle
1 - 1 of 1
Loading...
- Name:
- license.txt
- Size:
- 1.71 KB
- Format:
- Item-specific license agreed to upon submission
- Description:
