TARBIYYA A KARIN MAGANAR BAHAUSHE
Loading...
Date
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGE
Abstract
TSAKURE
Wannan bincike mai taken “Tarbiyya a Karin Maganar Bahaushe” aiki
ne da ya kalli karin maganganun Hausa a matsayinsu na makarantar tarbiyyar
Hausawa manya da qanana. An karkasa kundin zuwa babi shida. Babi na
xaya, gabatarwa ce ta gaba xayan aikin. A cikinsa aka bayyana manufar
bincike da muhallin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike tare da
ra’in da aka xora aikin a kansa. Babi na biyu ya yi bitar ayyukan da suka
gabata sannan da hujjar cigaba da bincike. Babi na uku ya yi waiwaye a kan
ma’anar tarbiyya da muhimmancinta da kuma hanyoyin tarbiyyar Bahaushe
na gargajiya da na zamani. Haka kuma, babin ya kalli ma’anar karin magana
da nau’o’inta da kuma muhimmancinta ga rayuwar Bahaushe. A babi na
huxu, nazarin ya kawo tarbiyyar yara a cikin karin maganar Hausawa. An
tattauna a kan haquri da gaskiya da kunya da addini da hali da alheri da
amana da ladabi da biyayya da tsoratarwa da yarinta da tunani, sannan aka
kawo misalan karin magana masu nuni ga kowane xaya daga cikinsu. Babi na
biyar ya kalli tarbiyyar manya a cikin karin maganar Hausa. An tattauna a kan
sana’a da zamantakewa da hankali da aure da haihuwa da mutuwa da zaman
lafiya da tunani da kyautatawa da kuma zumunci. Haka kuma, an kawo
misalai daga karin maganar Hausa masu nuni ga tarbiyya a cikinsu. Babi na
shida shi ne na qarshe, inda a cikinsa aka taqaita binciken sannan aka
kammala shi.
ABSTRACT
This research titled “Morality in Hausa Proverbs” dwelled into the study
of Hausa proverbs as tools used in transforming the behavior and morality of
both young and grown in Hausa society. The research is divided into six
chapters. Chapter one is the general introduction, which dealt with aim of the
study, as well as the scope and research methodology. The theory upon which
this work is based is also discussed in this chapter. Chapter two is a general
review on the related literatures. Chapter three revisited the meaning of moral
behavior and its importance. The chapter also reviewed the meaning of
proverbs, its types and importance to Hausa people, as well as conventional
and contemporary ways of instilling moral behavior in the Hausa society.
Chapters four and five studied Hausa proverbs that are used in teaching and
inculcating moral behavior to the young and grown respectively. The chapters
also gave ample examples of proverbs used in disseminating moral behavior in
Hausa customs. Chapter six is the last chapter; it presented summary and
conclusion to this research.
