TARBIYYA A KARIN MAGANAR BAHAUSHE

dc.contributor.authorAISHATU YAHAYA ADM. NO: 12210106002
dc.date.accessioned2026-03-05T10:01:06Z
dc.date.issued2018-09-23
dc.description.abstractTSAKURE Wannan bincike mai taken “Tarbiyya a Karin Maganar Bahaushe” aiki ne da ya kalli karin maganganun Hausa a matsayinsu na makarantar tarbiyyar Hausawa manya da qanana. An karkasa kundin zuwa babi shida. Babi na xaya, gabatarwa ce ta gaba xayan aikin. A cikinsa aka bayyana manufar bincike da muhallin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike tare da ra’in da aka xora aikin a kansa. Babi na biyu ya yi bitar ayyukan da suka gabata sannan da hujjar cigaba da bincike. Babi na uku ya yi waiwaye a kan ma’anar tarbiyya da muhimmancinta da kuma hanyoyin tarbiyyar Bahaushe na gargajiya da na zamani. Haka kuma, babin ya kalli ma’anar karin magana da nau’o’inta da kuma muhimmancinta ga rayuwar Bahaushe. A babi na huxu, nazarin ya kawo tarbiyyar yara a cikin karin maganar Hausawa. An tattauna a kan haquri da gaskiya da kunya da addini da hali da alheri da amana da ladabi da biyayya da tsoratarwa da yarinta da tunani, sannan aka kawo misalan karin magana masu nuni ga kowane xaya daga cikinsu. Babi na biyar ya kalli tarbiyyar manya a cikin karin maganar Hausa. An tattauna a kan sana’a da zamantakewa da hankali da aure da haihuwa da mutuwa da zaman lafiya da tunani da kyautatawa da kuma zumunci. Haka kuma, an kawo misalai daga karin maganar Hausa masu nuni ga tarbiyya a cikinsu. Babi na shida shi ne na qarshe, inda a cikinsa aka taqaita binciken sannan aka kammala shi. ABSTRACT This research titled “Morality in Hausa Proverbs” dwelled into the study of Hausa proverbs as tools used in transforming the behavior and morality of both young and grown in Hausa society. The research is divided into six chapters. Chapter one is the general introduction, which dealt with aim of the study, as well as the scope and research methodology. The theory upon which this work is based is also discussed in this chapter. Chapter two is a general review on the related literatures. Chapter three revisited the meaning of moral behavior and its importance. The chapter also reviewed the meaning of proverbs, its types and importance to Hausa people, as well as conventional and contemporary ways of instilling moral behavior in the Hausa society. Chapters four and five studied Hausa proverbs that are used in teaching and inculcating moral behavior to the young and grown respectively. The chapters also gave ample examples of proverbs used in disseminating moral behavior in Hausa customs. Chapter six is the last chapter; it presented summary and conclusion to this research.
dc.identifier.urihttps://repository.udusok.edu.ng/handle/123456789/362
dc.language.isoother
dc.publisherDEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGE
dc.titleTARBIYYA A KARIN MAGANAR BAHAUSHE
dc.typeOther

Files

Original bundle

Now showing 1 - 1 of 1
Loading...
Thumbnail Image
Name:
Tarbiyya A Karin Maganar Bahaushe.pdf
Size:
784.37 KB
Format:
Adobe Portable Document Format

License bundle

Now showing 1 - 1 of 1
Loading...
Thumbnail Image
Name:
license.txt
Size:
1.71 KB
Format:
Item-specific license agreed to upon submission
Description: